Sa’o’i kadan da sace ma’aikatan karamar hukumar Zariya da ‘yan-bindiga su ka yi, gamayyar kungiyoyin Arewa ta bada kashedin karshe game da hauhawar hare-haren ‘yan-bindiga da ta ce abun ya isa haka.
A yammacin Litinin ne dai ‘yan-bindigan da ke yankin karamar hukumar Giwa a jahar Kaduna su ka tare motar ma’aikatan karamar hukumar Zariya wadanda su ka kai ziyarar ta’aziyya inda su ka sace mutane 18 daga ciki.
Ganin yadda sace-sacen mutanen ke sake sabon salo ne, ya sa gamayyar kungiyoyin Arewa reshen dalibai, ta ce tura-ta-kai-bangon da za ta dauki irin na ta mataki, inji babban jami’in kungiyar na Jahar Kaduna Kwamred Jamilu Musa.
Mai nazari kan al’amuran yau da kullun Alhaji Abubakar Umar Aliyu ya ce sace wadannan ma’aikatan ya nuna gwamnati ta gaza amma kuma akwai mafita.
Matsayin gwamnatin jahar Kaduna kan ‘yan-bindiga dai shine ba sulhu sai dai kuma gwamna Nasiru Ahmed El-Rufa’i ya sha nanata cewa jami’an tsaro na kokari gameda wannan batu.
Yanzu haka dai ‘yan-uwa da abokan arzikin ma’aikatan da aka sace na ta faman juyayi a yayin da gwamnatin jahar Kaduna ba ta ce uffan kan batun ba tukuna.