X

Yadda aka kashe ƴan sanda 13 a jihar Zamfara

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar jami’anta 13 a ƙauyen Kurar Mota na Karamar Hukumar Bungudu a jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya

Rundunar ta tabbatar da faruwar lamarin ne a wata sanarwa da ta fitar wa manema labarar a ranar Lahadi, inda take cewa kisan jami’an ƴan sandan ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 12.30 na dare.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da jami’an suka amsa kiran kai daukin gaggawa kan yunƙurin kai farmaki a ƙauyukan da ke kusa a yankin karamar hukumar.

Sanarwar wacce kakakin rundunar ‘yan sandan Mohammed Shehu ya fitar ta ce “Jami’an ‘yan sanda 13 sun rasa rayukansu a bakin aiki, amma kuma su ma ‘yan fashin dajin sun samu munanan raunuka”.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara ta yi alwashin cewa faruwar lamarain ba zai sanyaya gwuiwar jami’anta wajen gudanar da aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin jama’a ba,” in ji sanarwar.

Ta kuma yi kira fa duk wani dan kasa bai bin doka da su bai wa jami’an tsaro hadin kai wajen tabbatar da samun nasarar kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi jihar.

Da farko dai in ji mazauna yankin da suka shaida wa manema labarai, ‘yan bindigar sun yi yunƙurin kai farmaki a ƙauyen Magami, mai nisan kilomita 50 daga kudancin Gusau babban birnin jihar amma sojoji suka fatattake su.

“Amma kuma sun abka wa wani ƙauye da ke tsakanin hanyoyin ƙauyukan Magami da Dankurmi da kuma Dangulbu inda suka banka wa shaguna huɗu wuta tare da hallaka mutum guda”.

Daga nan ne suka abkawa ƙauyen na Kurar Mota inda suka kai hari kan caji ofis na ‘yan sandan da ke kusa da dakin shan magani.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings