Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya kira taron gaggawa sakamakon tabarbarewar tsaro a babban birnin kasar.
‘Yan bindiga sun yi ta kutsawa cikin gidaje tare da daukar mazauna dake cikin kwanciyar hankali a gidajensu.
Lamarin da ya haifar da tashin hankali ya kai inda aka kashe wasu mazauna yankin ciki har da wata dalibar Sakandare mai shekaru 13 saboda rashin cika wa’adin biyan kudin fansa.
Da yake jawabi a taron, wanda ke gudana, Wike ya tabbatar wa mazauna FCT cewa an tabbatar da tsaron lafiyar su.
Ya ce gwamnati na kokarin tallafa wa jami’an tsaro da duk abin da suke bukata domin magance matsalar rashin tsaro.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugabannin hukumomin tsaro a babban birnin tarayya Abuja, manyan jami’an hukumar babban birnin tarayya (FCTA), shugabannin kansiloli da kuma sarakunan gargajiya.
Wike ya gargadi shuwagabannin kansilolin yankin da su kasance a raye da alhakin da ya rataya a wuyansu a matakin kananan hukumomi
Ya kuma jaddada bukatar jami’an tsaro su sake yin dabara tare da rubanya kokarinsu na ganin an shawo kan matsalar rashin tsaro a yankin.
“Dukkanmu muna sane da matsalar tsaro a babban birnin tarayya, musamman Bwari da wasu yankunan da suka fuskanci kalubale. Ina sane da cewa, a wasu lokutan, ‘yan jarida su kan tozarta abin da ke faruwa, amma duk sun damu da babban birnin tarayya, kusan kowane dan Nijeriya zai zama wajibi ya tabbatar da cewa wurin ya kasance lafiya, muna yin duk abin da za mu iya kuma muna tabbatar wa ‘yan Nijeriya mazauna. a nan cewa babu bukatar firgita.
“Muna daukar kowane mataki don tabbatar da cewa an warware wadannan kalubale; don haka wannan taron a zahiri shine don duba irin waɗannan ƙalubalen don ganin yadda za mu iya magance su. Don haka ne muka gayyato daukacin shugabannin kansilolin domin su ma suna da nauyi a majalissu daban-daban, don haka ya zama wajibi mu hada hannu wajen samar da mafita.