Wata kungiyar kare hakkin dan-Adam tana shirin kai karar Faransa gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya domin neman diyya a kan wadanda gwajin makamin nukiliya da ta yi a kasar ya shafa a shekarun 1960.
Kungiyar fafutukar kawo karshen makaman nukiliya ta duniya a Algeria ta yi ikirarin cewa mutane da dama sun yi fama da cutuka na daji da sauransu sakamakon gwajin makaman nukiliya tsawon shekara shida a kasar.
Kungiyar ta ce gwamnatin Faransa ta yi burus ta ki amsa bukatar da kungiyar ta yi ta gabatar mata ta neman ta biya diyya ga wadanda abin ya shafa.
Shugaban Algeria, Abdelmadjid Tebboune, ya goyi bayan neman biyan diyyar.