Akalla mutane takwas ne ciki har da jariri dan watanni takwas aka kashe a unguwar Farin Lamba da ke gundumar Vwang ta karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.
Wannan harin ya faru ne a unguwar Sabon Gari dake karamar hukumar Mangu ta jihar inda aka ce an yi asarar rayuka da dama tare da kona gidaje kwanaki biyu da suka wuce.
A cewar Rwang Tengwong, sakataren yada labarai na kungiyar Berom Youth Mooulders, maharan sun isa unguwar ne da misalin karfe 9:45 na yammacin ranar Lahadi a lokacin da yawancin al’ummar yankin ke barci.
Ya ce, “da misalin karfe 9:45 na daren Lahadi, 09/10/2023, wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane takwas ciki har da jariri dan wata takwas a Farin Lamba, gundumar Vwang ta karamar hukumar Jos ta Kudu.
“’Yan bindigar sun ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba a wasu al’ummomin kananan hukumomin Riyom, Barkin Ladi, Jos ta Kudu da Mangu na jihar Filato, a wani sabon harin da aka sake kai wa a babban zaben 2023.
“Jaririyar da aka kashe tare da Mahaifiyar ta an ce tana dawowa daga asibiti a lokacin da suka gamu da ajalinsu. Kafin wannan harin na rashin imani, wasu al’ummomi a kananan hukumomin Riyom, Barkin Ladi, Jos ta Kudu da Mangu sun shaida yadda aka lalata gonaki da gangan da kuma kiwo sama da hekta 300.
“Har ila yau, a kullum ana yin kwanton bauna tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a karamar hukumar Riyom, daura da babbar hanyar Abuja.
“BYM karkashin jagorancin Solomon Dalyop Mwantiri, Esq. don haka ya yi Allah-wadai da harin da kuma tada zaune tsaye da aka kai wa wadanda ba su ji ba ba su gani ba a Filato tun bayan zaben 2023,” in ji shi.
Sai dai kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) a jihar ta ce ba ta da masaniya kan harin da aka kai a yankin.
Nuru Abdullahi, shugaban kungiyar MACBAN na jihar ya ce, “ba mu da masaniyar zargin da ake mana. A duk lokacin da aka ci abinci, ana zargin al’ummar Fulani. Don haka, wannan ba sabon abu ba ne a gare mu. Dangane da abin da ya shafi MACBAN, zargin yaudara ne.”
Sai dai kungiyar, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, DSP Alabo Alfred, bai amsa kiran da kuma sakon da wakilinmu ya aike kan lamarin ba har zuwa lokacin hada rahoton.
domin a tura karin ma’aikata domin yin aiki da Al’umma a kananan hukumomin Barkin Ladi da Jos ta Kudu.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, DSP Alabo Alfred, bai amsa kiran da kuma sakon da wakilinmu ya aike kan lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.