Wasu manoman tumatur a karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano, sun koka kan yadda tsutsa ke lalata musu amfanin gona.
Manoman sun ce sun yi asarar amfanin gona da ta kai kusan Naira miliyan 500.
Sun kuma ce tsutsar ta shafi kusan hekta 1000 na gonakinsu.
Wani manomin tumatir, Bello Idris ya ce suna cikin wahalhalu kan yadda tsutsar ta addabe su.
”Za mu nome tumatir mu sayi taki 50,000, mu kuma sayi maganin feshi 10,000 da man fetur amma duk a banza,” in ji shi.
Ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki da kuma gano inda matsalar take.
Haka-zalika, shi ma Sama’ila Bello mazaunin karamar hukumar Dawakin Tofa, ya ce tsutsar na lalata musu amfanin gona cikin lokaci kankani.
“Muna so gwamnati ta taimaka mana a duba a ɓangaren iri ne ko maganin feshi ne ba a sayar da mai kyau,” in ji Bello.
BBC Hausa