Wata kotu a birnin Abuja dake Najeriya ta yanke hukuncin cewar dauke tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu daga Kano zuwa Nasarawa bayan tube shi daga karagar mulki ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2020 ya saba ka’ida.
Mai shari’a a kotun Anwuli Chikere yayin yanke hukuncin tace dokar Majalisar Masarautar ta shekarar 2019 da gwamnatin Jihar Kano tayi amfani da ita wajen kai Sarki Sanusi Jihar Nasarawa ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.
Chikere tace kundin tsarin mulkin Najeriya ya fi karfin duk wata doka da akayi, saboda haka tsohon Sarkin na da hurumin zama inda yake so a Najeriya ciki harda Jihar Kano kamar yadda kundin tsarin mulki ya bashi dama.
Kotun ta baiwa gwamnatin Jihar Kano da Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya da Darakta Janar na Hukumar DSS umurnin biyan diyyar naira miliyan 10 da kuma neman gafarar tsohon Sarkin a cikin manyan jaridun kasar guda 2.
Sarki Sanusi ya shigar da karar ce inda ya bukaci kotu da ta haramta tsare shi da akayi wanda ya sabawa yancin sa da kuma dauke shi daga Kano.
Wannan ya biyo bayan sauke shi daga karagar mulki a matsayin Sarkin Kano na 14 da gwamnatin jihar Kano a karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tayi, inda ta maye gurbin sa da Sarki Aminu Ado Bayero.
Sarki Sanusi bai kalubalanci sauke shi daga karagar mulki da gwamnatin jihar Kano tayi a gaban kotun ba, kuma ita ma kotun bata ce komai akan raba shi da sarautar ba.