X

Tanzania ta haramta wa matan da suka haihu zuwa aji da jarirai

Ministan ilimi na Tanzania Adolf Mkenda ya ce matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na barin ɗalibai mata su ci gaba da zuwa makaranta bayan sun haihu ba yana nufin su rinƙa zuwa da jariransu bane.

Batun nashi na zuwa ne bayan wani rahoto da ya nuna wata uwa a yankin Mbeya da ta je da jinjirarta ƴar wata huɗu aji a makon nan.

Jaridar BBC ta wallafa a shafinta cewa Esnath Gideon mai shekara 19 na zaune a cikin aji ɗauke da ƴarta inda ta shaida wa BBC cewa dole ne ta sa ta je da jinjirarta aji sakamakon babu wanda zai taimake ta ya yi mata raino a gida.

Sai dai Farfesa Mkenda ya ce zuwa da jarirai aji zai rinƙa damun sauran ɗalibai.

A baya dai ɗalibai ƴan makaranta da suka ɗauki ciki a Tanzania ana korarsu daga makarantu kuma ba a barinsu su dawo, sai dai wannan dokar da aka shafe shekara 19 ana amfani da ita an soke ta a Disambar bara, wanda hakan ya sa mata da yawa suka koma makaranta domin kammala karatunsu.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings