Site icon TWINS EMPIRE

SUPER FALCONS SUN LASHE GASAR WAFCON – KARON SU NA 10 A AFRIKA

Ƙungiyar mata ta ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Falcons, sun sake kafa tarihi ta hanyar lashe kofin WAFCON karo na goma bayan doke Morocco 3–2 a wasan ƙarshe. Najeriya ta yi nasarar ne bayan ta bi baya da kwallaye biyu, kafin ta dawo da ƙarfi ta ci kwallaye uku, a cikin wani comeback mai ban mamaki.

Ƙwallon da ta sauya wasan ta fito daga fitacciyar ‘yar wasan gaba, Esther Okoronkwo, wadda aka bayyana a matsayin MVP (mafi fice a gasar). Koci Randy Waldrum ya yi canje-canje masu kyau da taimaka wa kungiyar ta sake samun daidaito da ƙarfi.

Wannan nasara ta tabbatar da Najeriya a matsayin shugabar ƙwallon ƙafa ta mata a nahiyar Afirka, inda ta lashe kofin fiye da kowace kasa. Super Falcons sun bayyana cewa wannan nasara ce ga ‘yan Najeriya da ke fuskantar ƙalubale a gida.

Exit mobile version