Gwamnatin jihar Kano ta ce hukuncin da wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ta yanke a safiyar ranar Alhamis, ya nuna cewa har yanzu Alhaji Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano.
Babban Lauyan jihar kuma kwamishinan shari’a Barista Haruna Isah Dederi ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidan gwamnati da yammacin Alhamis.
Ya ce, “A yau 20 ga watan Yuni, 2024, babbar kotun tarayya mai lamba 1, Kano ta yanke hukunci kan karar da ke gabanta. Ina da farin ciki a madadin Mai Girma Gwamna Abba K. Yusuf da Gwamnatin Jihar Kano, da in sake yi muku jawabi kan shari’ar da ta kunno kai dangane da soke masarautu biyar da tsige tsoffin sarakuna. (ciki har da hambararren sarkin kananan hukumomi 8). Gwamnatin jihar Kano ta amince da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke game da dokar majalisar masarautar Kano ta shekarar 2024 tare da ganin ta tabbatar da doka.
“A bisa hukuncin da Kotu ta yanke, babu shakka. ya kara tabbatar da ingancin dokar da majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ita kuma mai girma gwamnan jihar Kano a ranar Alhamis 23 ga Mayu, 2024 da karfe 5:10 na yamma ya sa hannu. Wannan bangare na shari’ar yana da matukar muhimmanci ga dukkan lamarin.
“Ƙarin ma’anar hukuncin shi ne, duk ayyukan da Gwamnati ta yi kafin fitowar umarnin wucin gadi na Kotun Mai Girma, sun tabbata daidai da haka. Wannan yana nufin cewa, soke masarautu biyar da aka yi a shekarar 2019 ya tabbata kuma an tabbatar da tsige sarakunan biyar da babbar kotun tarayya ta yi. Ma’ana wannan yana nufin Muhammadu Sanusi II ya ci gaba da zama sarkin Kano.
“Alkalin ya kuma amince da bukatar mu na a dage shari’ar har sai kotun daukaka kara ta yi shari’ar daukaka karar da ke gabanta kan hurumin shari’a. Abin farin ciki, an rattaba hannu kan wannan doka tare da mayar da Mai Martaba Sarki Muhammad Sunusi II kan mukaminsa a ranar 23 ga Mayu, 2024 kafin fitowar dokar wucin gadi wadda aka ba mu a ranar Litinin 27 ga Mayu, 2024.”