Wani kasurgumin dan fashi da makami mai suna Abdulkareem Lawal da ake kira Faca-faca, da mabiyansa da dama sun rasa rayukansu a wani harin da sojojin saman Najeriya suka kai ta sama…
Wani kasurgumin dan fashin nan mai suna Abdulkareem Lawal da ake kira Faca-faca, tare da dimbin mabiyansa sun rasa rayukansu a wani hari da jiragen yakin sojin saman Najeriya suka kai wa wasu gungun ‘yan bindiga a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Wakilinmu ya samu labarin cewa an kai harin ne da yamma.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah, ya tabbatar a ranar Lahadin da ta gabata cewa an kashe wasu da ake zargin ‘yan fashi ne guda takwas da suka hada da Faca-faca a yayin farmakin.
Ya kuma ce a daren ranar Asabar ne ‘yan sandan suka kai farmaki maboyar ‘yan ta’adda a Unguwar Dako, kauyen Tandama da ke karamar hukumar Danja a jihar inda suka kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su.
Isah ya bayyana sunayen wadanda aka ceto kamar yadda Alhaji Garba DanMallam mai shekaru 52; Rabiu Idris, 45; da Abba Samaila mai shekaru 38, wadanda dukkansu mazauna Unguwar Nuhu ne.
Sauran su ne Yunusa Sani mai shekaru 54; Ishaq Yakubu, 40; da Danjuma Samaila mai shekaru 45, dukkansu mazauna kauyen Layin Sani, Kafur.
A halin da ake ciki kuma, ‘yan bindiga sun kashe wasu ‘yan banga guda biyu tare da yin garkuwa da wasu sabbin aure da wasu mazauna unguwar Shola Quarters a cikin birnin Katsina.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun mamaye yankin ne da misalin karfe 1:25 na safe inda suka kwashe sama da awa daya suna aikin.
Daya daga cikin majiyar ta ce, “’yan banga ne har sun fuskanci ‘yan bindigar, amma ana cikin haka, an kashe biyu daga cikinsu, wasu biyu kuma suka jikkata.”
Ya bayyana cewa ‘yan banga sun ja da baya domin kare lafiyarsu lokacin da ‘yan fashin suka ci karfinsu.
Ya ce daga baya ne aka dauko gawa daya yayin da daya daga cikin wadanda suka jikkata aka garzaya da su asibiti ya mutu.
Da yake bayyana yadda aka yi garkuwa da sabbin ma’auratan, wani dan uwa Usman Masanawa, ya ce mijin Yusuf Bishir ya kira shi ya sanar da shi harin amma babu abin da zai iya yi.
“Mun je can da safiyar yau; ‘Yan fashin ba su ma shiga gidan ta kofar shiga ba amma sai suka farfasa katanga suka shiga gidan,” in ji Masanawa.
Ya kara da cewa ba za a iya tantance adadin mutanen da aka sace ba amma wasu mazauna yankin sun ce an kai wa wasu gidaje hari tare da sace mutane.
Lokacin da aka tuntube shi, PPRO wanda ya amsa ta sakon WhatsApp, ya ce jami’an na kan aiki (kan lamarin) kuma za su yi bayani dalla-dalla daga baya.
A wani harin kuma, wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 13 daga kauyen Natsinta da ke karamar hukumar Jibia, wanda ke da tazarar mitoci kadan daga barikin sojoji a Katsina.
Wani mazaunin garin da aka yi garkuwa da kawunsa da ’ya’yansa biyu, ya ce a baya ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutane 26 amma da suka isa inda suka ajiye babura suka tafi da 13 tare da barin sauran.