Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK), sun bayyana cewa sun ceto wata ‘yar makarantar Chibok a jihar Borno.
Yarinyar da aka ceto na daga cikin ‘yan matan makaranta 276 da Boko Haram suka sace a ranar 14 ga Afrilu, 2014 a garin Chibok.
An bayyana hakan, jiya ta bakin Theatre Commander, na OPHK, Maj-Gen. Gold Chibuisi, yayin da yake mika Mary Nkeki ga kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Borno, Zuwaira Gambo a unguwar Maimalari dake Maiduguri.
Ya ce an ceto Mary, mai shekaru 27, a ranar 14 ga watan Agusta, 2023, daga hannun sojojin bataliya ta 81 ta Najeriya, Dikwa, wata al’umma da ke kan iyaka da Kamaru.
Ya kuma bayyana cewa sunan Maryam yana lamba ta 55 daga cikin jerin sunayen ‘yan matan makarantar Chibok da aka sace a watan Afrilun 2014.
“Sojojin mu ne suka ceto Maryam, yayin da daya Adamu; Mijinta ya mika wuya ga Sojoji a makon da ya gabata a yankunan kan iyakar Kamaru,” in ji Chibuisi kan yadda aka ceto.
Wakilinmu ya tattaro cewa Maryam tana da jarirai guda biyu tare da mijinta, amma sun mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki mai tsanani (SAM) a dajin Gulumba na karamar hukumar Bama.
Ta bayyana cewa, duk da ceton da ta yi, tana so ta sake haduwa da mijinta, Adamu, wanda tuni ya mika wuya a makon jiya a Dikwa.