X

Sojoji sun ceto mutum 669 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su

Akalla mutum 669 aka ceto daga hannun wadanda ke garkuwa da su cikin mako uku da ya gabata, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Shakwatar tsaro ta sojojin Najeriya (DHQ) ta ce an kashe mayaka da ‘yan bindiga 23, kuma an kama 19 sannan mayaka 1,158 tare da iyalansu sun mika kawunansu ga dakarun Najeriya.

Babban jami’i mai kula da harkokin yada labarai na rundunar sojojin Najeriya, Manjo-Janar Bernard Onyeuko, ya ce “dakarun kasar sun kuma kama wani Abdurrazaq Hudu wanda ya ce yana sayar wa kungiyar ISWAP kayayyakin yaki ne, inda aka kama shi a Mutum Biyu da ke karamar hkumar Gassol ta jihar Taraba.

Manjo-Janar Onyeuko ya ce cikin mutum 1,158 din, akwai maza 164 da mata 367 da kuma yara 627.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings