X

SOJIN SAMAN NIGERIA SUN SAMU NASARA AKAN YAN TADA KAYAN BAYA

Rundunar Sojojin saman Nijeriya NAF, bangaren dakarun ‘Operation LAFIYA DOLE’ ta wargaza wani sansanin shirya ayyukan kai hare-hare na ‘yan kungiyar son kafa daular Islama ta Yammacin Afirka (ISWAP) tare da kashe mayakansu da dama a wani harin sama da a ka zartar a Tumbun Rego da ke kan gabar Tafkin Chadi a jihar Borno.

Jami’in yada labarai na Hedikwatar Tsaro ta Kasa, Manjo Janar John Enenche, ne bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu cikin makon nan, a inda ya ke cewa, an aiwatar da harin ne a ranar 22 ga Nuwamba, 2020, a bisa wasu rahotannin sirri na sahihan bayanai da ke nuna cewa, wurin tare da gine-ginensa ‘yan ta’addan su na amfani da shi ne a matsayin matattarar kayan aikinsu da su ke a jiye wa kafin su yi sufurar su ta tafki ta hanyar amfani da manyan motoci da babura.

Don haka ne rundunar sojin sama ta aika da jiragen yaki na sojojin saman Nijeriya (NAF) da jiragen yaki masu saukar ungulu, don kai hari a wurin.

A yankin da a ka kai harin, an lura da cewa, akwai muhimman abubuwan ISWAP, a inda su ka shagalta suna ganin cewa jirgin saman NAF wucewa kawai zai, wanda hakan ya haifar da lalata tsarin ta’addancinsu tare da kawar da yawancin mayakansu.

Babban kwamandan sojan ya yaba wa rundunar Sojin sama bisa kwarewar da su ka nuna, sannan ya kuma bukace su da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu, domin kawar dukkan wasu ‘yan ta’adda a kasar nan.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings