X

Shugaban Zambia ya sauya manyan hafsoshin tsaron kasar

Sabon shugaban Zambia Hakainde Hichilema ya sauya manyan hafsoshin sojin kasar da na ‘yan sanda – hakan na nuna cewa zai fi mayar da hankali kan inganta tsaron kasar.

A ranar Lahadi shugaban ya sanar da sunayen sabbin hafsoshi a rundunar sojin kasa na Zambia da kuma na sama da kuma sabon babban sufeton ‘yan sanda na kasa.

Hakazalika an sauke dukkanin kwamishinonin ‘yan sanda sai dai ba a bayyana wadanda za su maye gurbinsu ba.

Mr Hichilema ya ce dole sabbin nade-naden da ya yi su kasance masu kishin kasa da kare hakkin bil adama da ‘yan ci da walwala.

Sannan ya yi kira ga ‘yan sanda su mayar da hankali wajen kawar da bata-gari da binciker wadanda ake zargi da laifuka.

Mr Hichilema, wanda ya hau mulki bayan nasara a zaben da aka gudanar cikin wannan watan, ya taba fuskantar cin zarafi a hannun ‘yan sanda.

An sha kama shi da daure shi – kuma ya yi alkawarin yaki da wannan dabi’a – da sauya yadda jami’an tsaro ke aiki.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings