X

Shugaba Putin na Rasha ya zargi Amurka da neman jefa kasarsa yaki a Ukraine

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya zargi Amurka da neman jefa kasarsa yaki a Ukraine.

Ya ce manufar Amurka ita ce ta fake da sa-in-sar da ake ta yi domin ta kara sanya wa kasarsa Rasha.

Mista Putin ya kuma ce Amurka na kawar da kai a kan damuwar da Rasha ke nunawa kan kawancen sojojin kungiyar Nato a Turai.

Amurka da kawayenta na Nato na zargin Rasha da shirin mamayar Ukraine, abin da Rasha ta musanta.

A jiya Talata sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fitar da wani sako na tuwita cewa Amurka ba ta da wani wuri na tayar da yakin da ba wanda yake kaua.

A ‘yan makonnin nan Rasha ta tura dakarunta kusan dubu dari, hade da duk wani kayan yaki da za su bukata zuwa iyakarta da Ukraine.

Rashar ta yi hakan ne shekara takwas bayan ta mamaye tsibirin Crimea da ke kudancin Ukraine, ta kuma goyi bayan kazamin juyin mulkin da aka yi wanda aka zubar da jini a yankin gabashin Donbas.

Da yake magana da Firaministan Hungary Viktor Orban a Moscow, Mista Putin ya ce, yana ganin Amurka ba ta damu da tsaron Ukraine ba, babban burinta shi ne ta dakile ci-gaban Rasha, ta hanyar fakewa da wannan rikici.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings