Shekaru 15 kenan da zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan Saddam Hussein, bayan da kotu ta same shi da laifin aikata kisan kare dangi a kan ‘yan kasarsa.
Shekaru 15 kenan bayan mutuwarsa bayan da wata kotu a Iraki ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan Saddam Hussein, har yanzu ‘yan kasar ta Iraki na ci gaba da tunawa da mulkinsa na tsawon shekaru fiye da 30.
Kamar yadda kafofin watsa labarai na duniya a ranar 30 ga watan Disamba na shekarar 2006 suka yada, an ga marigayi Saddam Hussein din na kalmar shahada a lokacin da yake fadawa cikin ramin da ke karkashin daben ratayeshi.
An kuma jiyo masu daure shi, na rera taken batanci da mummunar addua’a ga marigayin, lamarin da ke jawo tababa kan sahihancin shari’ar da aka yi masa. Lauyoyin Saddam na zargin cewa, anyi masa shari’ar mugunta da neman daukar fansa ne, kuma dukkani kokarinsu na neman daukaka kara ya ci tura.
Su kansu kasashen Larabawa, ciki har da kasar Kuwait da ya mamaye ta a shekarar 1990, sun nemi da ayi mar afuwa, kodayake, sabin mahukuntan Iraki da suka zartar masa da hukuncin, sunce Larabawan sun yi hakanne don gudun kar a bude kofar rataye shuwagabannin kama karya a yankin.
Amirka ta mika Saddam ga gwamnatin Nuril Maliki, wacce ba zabarta aka yi ba, duk da cewa ta san shi mai matsanancin ra’ayin Shi’anci ne da kuma kanzagi ga kasar Iran da ke neman ganin bayan Saddam ko ana ha maza ha mata, kuma Amirkan tayi haka ne don a dokance, Saddam Hussein,a wurinta firsinan yaki ne da bata da hurumin yanke masa hukuncin kisa, lamarin da ke nuni da yadda makarkashiyar da aka kitsa dangane da yanke hukuncin rataya ga marigayi Saddam din.
Tun bayan zartar da hukuncin rataya ga Saddam din, Shekaru 15 da suka gabata, kasar ta Iraki ta tsunduma cikin halin zaman kara zube da tashe-tashen hankali, gami da karuwar talauci ,yadda ake zargin sabin shuwagabanin da suka biyo bayan Saddam din da gudanar da mulkin kabilanci da nuna bambamcin akidar addini gami da dukufa wajan watandar da arzikin kasa.