Shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe na jihar Kano Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya bayyana cewa tsohon Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sha sanya shi ya binciki dan takarar Gwamnan jihar Kano a jam’iyyar APC Dr Nasiru Yusuf Gawuna.
A cewar Muhyi wani binciken daga cikin gidan Gwamna aka Turo shi, sai shi kuma Ganduje ya sa lallai sai an bincika.
Akwai lokacin da Gwamnati ta gididdiba wani gidan gona na Farm Center Kuma aka sa a kwashe kayan ciki, amma kuma daga baya sai tsohon Gwamnan da kansa kuma wai yasa na bincika da sunan wanda yake zargi.
A ƙalla sau uku Ganduje yana sani na binciki Dr Nasiru Yusuf Gawuna, shi isa da ya tsayar dashi takarar Gwamna na rinƙa dariya, saboda kana zargin mutum kuma ka tsayar dashi.
Anyi badaƙaloli da yawa a Gwamnatin baya, amma bazan faɗi wasu ba, wasu a rubuce za’a fito dasu dan a ƙwato wa al’ummar Kano haƙin su ~ inji Muhuyi Magaji Rimin Gado