Shugaba Joe Biden na Amurka ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da za ta iya wurin taimaka wa jihohin ƙasar shida da bala’in mahaukaciyar guguwa ta daidaita.
Mr Biden ya ayyana dokar ta ɓaci a Kentucky, inda rahotanni ke cewa sama da mutun 100 sun mutu sakamakon guguwa.
Garin Mayfield ne ya fi jin jiki a wannan bala’in, inda gine-gine suka rushe, haka gidaje da kuma coci-coci.
Ko a Illinois aƙalla mutun shida guguwar ta kashe, a lokacin da iska ya ruguza ginin ma’aikatar da suke ciki.
Shugaba Biden ya ce sun shirya bada agajin gaggawa ga ɗimbin mabuƙata, lura da cewa da dama sun rasa ruwan sha da wutar lantarki.
Rahotanni sun ce ko a jihohin Arkansas da Missouri da Tennessee an samu mace-mace, kuma yanzu haka guguwar ta afka wa Mississipi.