X

SAKACI DA GANGANCIN DA HUKUMOMI DA ALʻUMMA KE YI AKAN CUTAR CORONAVIRUS (COVID 19) YA NUNA HAR YANZU BAʻA FAHIMCE TA BA

Daga Mustapha Adamu Indabawa

Da farko bana son nace wani abu game da cutar coronavirus, amma irin riƙon sakainar kashi da naga alʻumarmu da mahukuntan mu na yi mata naga ya dace nace wani abu gwargwadon iko. Yau kimanin wata biyu kenan ina aiki akan wannan cuta. Dukkan ayyukan hukumar lafiya ta duniya (WHO) da ya danganci fassara zuwa harshen Hausa da tallace-tallacen radio da talabijin yana biyowa ta wajena kafin a bawa gidajen rediyo da talabijin su fara sakawa ko nunawa. Don haka zan iya tofa albarkacin baki na akan wannan masifa da ta same mu baki ɗaya tunda na karanta abubuwa da yawan gaske akan wannan cuta.

A ɓangaren sakaci irin na alúmar mu, na zagaya cikin birnin Kano naga rashin ababen hawa akan titunan mu, amma abin takaici da na shiga mahaifata Ƙofar ƊanʻAgundi sai na tarar da majalisu daban-daban mutane sun cakuɗu da juna ana ta zaman hira kamar ba waɗanda aka basu umarnin su zauna a gida ba. Na wuce wajen Makwarari na tarar gabaɗayan titin unguwar an mayar da shi filin ball. Daga nan na wuce Sharaɗa naga mutanen unguwar sun fito suna ta gyaran kwatami. Da na tambaye su meyasa basu zauna a gida ba suka fito suna cakuɗuwa da juna? Sai ɗaya daga cikinsu ya amsa da cewa zaman banza ne basa son yi don haka suka fito suna aiki.

Sannan a ɓangaren ibada, akwai masallatan jumaʻa da suka ƙi bin dokar da aka kafa suka gudanar da sallar jumaʻa. A wasu unguwannin kuma, wasu marasa jin maganae masu shegen taurin kai suka haɗu suka yi sallar jumaʻa. Amma dai rahotanni sun nuna an kama wasu daga cikin limaman da suka jagoranci waɗannan salloli duk da cewa wanda ya bada sallah a ƙofar Naʻisa mutanen unguwar sun tada tarzoma baʻa iya samu an kama shi ba. Idan mutane sun san abunda yake tunkararsu game da wannan cuta, da walllahi ko masallachin ƙofar gidansu da ake salloli biyar baza su fito ba ballantana masallachin jumaʻa.

Idan har Saudi Arabia zata soke Umrah da aikin Hajji, ta soke tarawih da tuhajjud, ta tilasatawa ʻyan ƙasarta zama a gida to ina ga Kano da mu har yanzu bamu fahimci ina muka sa gaba ba! A kullum muna yaudarar kanmu cewa ko Saudi Arabia bata kaimu addini ba, amma mun fi ko ina yawan ʻyan maɗigo da luwaɗi, da ʻyan daba da masu shaye-shaye. Tsoron kada a zage mu yasa mun ƙi mu fuskanci gaskiya domin aiki da ita. Ya zama wajibi mu faɗawa kanmu gaskiya don mu yi aiki da ita kuma mu daina yaudarar kanmu. Haka kuma bana jin akwai garin da ya kai mu yawan masu maula saboda talaucinmu da rashin aikin yi.

A ɓangaren hukuma kuma, sakacin da ake yi da wannan cuta yayi yawa ƙwarai da gaske. Komai rashin ilimin mutum zai iya fahimtar cewa gwamnati ba da gaske take yin yaƙi da wannan cutar ba. Babban misali anan shine wanda ya kawo wannan cuta Kano ya shigo Kano ne bayan an rufe shige da fice a Kano. Idan har da gaske gwamnati take yi da bai iya shigowa Kano ba har ya shafawa wasu mutane a waje. Amma abin mamaki bai shafawa iyalinsa ba ko ɗaya, kuma wannan mutum shine shugaban dattijai na jamʻiyar APC a Kano Municipal. Sannan kuma shi amini ne ga gwamnan jihar Kano.

Wani ƙarin babban sakaci da riƙon sakainar kasha da gwamnati take yiwa wannan harka ita ce ta a ɗauki jinin mutum don gwaji kuma a rabu da shi ya shiga cikin mutane ya cigaba da harkokinsa da kowa kafin sakamakon gwajin ya fito. Wannnan sakacin ne yasa aka ɗauki jinin wannan mutum da ya kawo ta kuma aka rabu da shi ya taho Kano. Sai da sakamakon gwajin sa ya nuna yana da ita sannan aka biyo shi ana neman sa bayan yayi dukkan ɓarnar da zai iya yiwa Kanawa. Bayan an same shi ya zayyana dukkan waɗanda zai iya tuna yayi muʻamala da su. Bayan ya zayyana su aka nemo su aka ɗauki jininsu suma aka rabu da su suka cigaba da shiga mutane.

Daga cikin mutanen da aka gwada an sami mutum biyar daga suma suna da ita. Sannan suma aka fara neman waɗanda suka yi cuɗanya da su aka ɗauki jininsu suma suka cigaba da harkokinsu. Matuƙar haka zaʻa riƙa yi wallahi baza ayi nasara a yaƙi da wannan cutar ba idan an yi niyar nasarar kenan. Idan kuwa dama niyar yaɗa ta ake da ita to shikenan sai abinda Allah Yayi don ko yanzu babu tsimi babu dabara. Dole ne hukuma ta killace duk wani wanda ake zargi da wannan cuta kafin sakamakon gwajinsa ya fito don ba kowa ne zai iya killace kansa ba tsakaninsa da Allah tunda yawan faɗar Allah yafi a baki kawai baʻa aikace ba.

Kira na ga alʻuma shine su zauna a gida cikin iyalinsu, banda fitowa waje ko zaman majalisa tunda cuɗanyar ita ce baʻa so. Idan muka sami sati biyu zuwa uku a killace bama cuɗanya da mutane cutar da kanta zata mutu kuma komai mugun tanadin da aka yi mana akanta. Sannan kuma duk wanda yaji alamun ciwon sarƙewar numfashi da yawan tari da atishawa ko zazzaɓi to ya kira hukuma domin a gwada shi da iyalansa don su samu kulawar da ta dace da wuri kuma akan lokaci. Ina son mutane su sani cewa sai suna da rai ko lafiya sannan zasu iya zuwa masallachi su yi sallah.

Kira na kuma ga hukuma shine su daina wasa da rayukan jamaʻa, su dubi Allah su riƙe amanar da Allah Ya ɗora a hannunsu. Ya kamata su killace duk wani mutum da ake da zargin yana da ita kafin gwajin jininsa ya fito. Idan yayi saʻa bashi da ita ba wani abu ba ne a sake shi ya tafi gida, idan kuma yana da ita shikenan baʻa yi sakaci an ƙyale shi ya cigaba da yaɗa ta ba. Sannan kuma idan an kira su ya kamata su riƙa zuwa domin yau a unguwar Gama tun ƙarfe 11 na safe ake kiransu da suzo su tafi da wani mara lafiya da ake zargin yazo da ita daga Lagos sun ƙi zuwa har zuwa ƙarfe 4 na yamma.

A ƙarshe nake son na bada haƙuri ga duk wani wanda rubutu na ya ɓata masa rai don ba niyya ta kenan ba. Manufa ta ita ce mutane su ƙaru da waɗannan bayanai nawa kuma su ɗauki matakin kare kansu. Nan ba da jimawa ba zan yi wani rubutun akan yadda mutane zasu kare kan su daga ɗaukar cutar corobavirus (COVID 19). Allah Yasa mu gama da duniya lafiya, Yasa mu daga cikin bayinSa nigari. Yasa mu cika da Imani. Allah Ya nisanta mu da duk wani abin ƙi ƙarami ko babba. Llah Ya bamu ikon gane gaskiya kuma mu bi ta. Ya kuma bamu ikon gane ƙarya kuma mu guje ta.

  • Mustapha Adamu Indabawa
Categories: Marubuta
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings