X

SADAKA

DAGA NASIR NID.

MARUBUCI NASIR CHIROMA (NID)

RASHIN BADA SADAKA YA ZAMA LAIFI…
(Wani rubutu da nayi shekaru 3, an sake tunamin shi)
Jiya da rana ina tafiya a cikin mota ta akan titin Beirut dake Kano. Sai na hadu da cinkoson ababan hawa a Junction din da zai hada ni da Ibrahim Taiwo Road, ina tsaye ina jiran Dan Karotan da yake bayar da hannu, ya kira mu, sai kawai wata almajira ta zo ta nemi na bata sadaka. Na sa hannu na dauki Naira Hamsin daga cikin wasu kudi da suka rage min, na mika mata. Hakan da nayi sai na ga wasu tarin almajirai sun yiyo kaina, na dauki ragowar canjin da ya rage min na mika musu. Abinda ya bani mamaki sai kawai naga wani Almajiri ya sheko aguje ya zo wajen ya na so na bashi bara.

Na dube shi na ce dashi yayi hakuri, ba ni da kudi. Nan take sai mutumin ya dau fada, wai yaya zance bani da kudi! Nayi ta ban baki, ya hakura mutum ya sake daukar zafi. Ya dube ni acikin mota yace da ni ” Kan cikin wannan motar zaka ce baka da kudi, wallahi kuji tsoron Allah” Ni dai na bashi hakuri na ja motata nayi gaba na barshi yana fada shi kadai. 
Na yi murmushi a raina na ce, Allah sarki wannan almajirin bai san halin da na ke ciki ba a lokacin, kila ma shi aljihunsa cike ya ke da kudi, ni kuwa babu ko sisi a aljihuna…

Categories: Marubuta
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings