Rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata wasu rahotannin da suka ce sojojin da ke bakin aikin tsaron Kwalejin Horon Sojoji ta NDA bacci suke lokacin da ƴan bindiga suka kai hari wanda ya kai ga kashe sojoji biyu da sace soja ɗaya.
Sanarwar da babban jami’in yaɗa labarai na rundunar sojin ya fitar Manjo Janar Benjamin Olufemi Sawyerr ya ce labarin da wasu jaridar Cable ta wallafa ba gaskiya ba ne inda ya ƙalubalanci jaridar ta bayar da shaidar da ke tabbatar da jami’an sojin suna bacci lokacin da ƴan bindigar suka kawo hari.
Labarin da ake yaɗawa na cewa bacci ya kwashi jami’an da ke kula da kamarori na tsaro lokacin da ƴan bindigar suka abka kwalejin NDA.
Ranar Talata ne ɓarayin suka shiga marantar ta NDA suka kashe sojoji biyu suka yi garkuwa da daya.Kuma tun a ranar rundunar sojan ta ce ta dukufa domin kwato sojan nata.
Wasu rahotannin kafafen yada labarai na Najeriya, da ba a tabbatar ba na cewaan tsinci gawar sojan nan da ‘yan fashi daji suka sace a kwalejin ta koyon aikin soji da ke Kaduna.
Rundunar sojin ta ce babban hafsan sojin Najeriya da hukumomin NDA sun kaddamar da bincike domin gano yadda har aka samu matsalar da ta ba ƴan bindiga damar shiga kwalejin.