Rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta ƙaryata rahotannin da suka ce an sace jami’anta 20 a wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a ofishin ƴan sanda a Buni Yadi cikin ƙaramar hukumar Gujba.
Rundunar Ƴan sandan ta kuma ƙaryata labarin cewa sojojin Najeriya sun kuɓutar da su.
“Labarin cewa an sace ƴan sanda 20 a Buni Yadi da kuma kuɓutar su labarin ƙarya ne, domin babu wani jami’i a garin Buni Yadi a ranar da aka ce an kai harin,” a cewar sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan Yobe ASP Dungus Abdulkarim ya fitar
Sai dai sanarwar ta tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga da ake tunanin Boko Haram ne ko kuma na Iswap sun kai hari ofishin ƴan sanda a Buni Yadi inda uska ƙona ofishin amma babu wanda aka kashe ko aka sace ko ya ɓata.