Kungiyar Real Madridd za ta dauki Leon Goretzka a badi, wanda kwantiranginsa zai kare a Bayern Munich in ji jaridar Bild.
Real Madrid ta saba daukar dan wasa daga Bayern Munich abokiyar hamayya, wadda ta dauki Tono Kroos kan fam miliyan 25, yanzu a bana ta kulla yarjejeniyar kaka biyar da David Alaba, wanda kwantiraginsa ya kare a karshen Yuni
Jaridar ta Jamus ta kara da cewar kungiyar ta Sifaniya ta sanarwa da Leon Goretzka za ta dauke shi a badi,, idan bai tsawaita yarjejeniyarsa da Bayern Munich ba.
Real Madrid tana daga cikin kungiyoyin da ke tsuke bakin aljihu, bayan da matsin tattalin arziki da kungiyoyi suka fada sakamakon bullar cutar korona.
Tuni dai Luka Modric, mai shekara 35, ya saka hannu kan tsawaita zamansa a Real kaka daya, ana kuma sa ran Toni Kroos, mai shekara 31, wanda ya yi ritaya daga buga wa Jamus wasa, zai ci gaba da taka leda a Madrid kaka biyu.
To sai dai kuma Bild din ta gargadi Real Madrid cewar ba ita kadai ke son daukar Goretzka ba.
Manchester United wadda za ta iya rasa Paul Pogba a bana ko kuma a badi, za ta iya zawarcin Goretzka.