Aisha, wadda ba sunanta na yanka kenan ba, ta shiga rudu tun bayan tasowarta zuwa farkon shekarar 2021 saboda irin tsangwamar da ta fuskanta a cikin al’umma sakamakon kasancewarta mata-maza.
To sai dai a ‘yan watannin baya gwamnatin jihar Kano ta share wa Aisha hawaye bayan da ta dauki nauyin yi mata aiki domin mayar da ita cikakkiyar mace.
Yanzu haka dai Aisha mai shekara 22 ta fara zuwa makarantar gaba da sakandare inda take karantar harsunan Turanci da Larabci a kwalejin ilimi ta jihar Kano, sabanin a baya inda Aisha ba ta iya shiga cikin jama’a.
Wani abun farin ciki a tattare da Aisha a yanzu haka shi ne yadda ta samu saurayin da zai aure ta.
” Insha Allahu nan ba da jimawa ba za mu yi aure saboda na samu saurayi. Ba kamar a baya ba lokacin da jama’a suke guje mini.
Akwai lokacin da har an sa min rana ma da wani amma da aka shaida masa cewa ga larurar da ke damu na sai aka zuga shi ya fasa.”
Yadda rayuwa ta kasance min kafin a mayar da ni cikakkiyar mace
“Ni dai an haife ni da al’aurar namiji da mace kuma mahaifana tun a lokacin suka so su nema min magani amma sakamakon rashin wadata hakan bai samu ba”, in ji Aisha.
Kasancewar ba a yi wa Aisha magani ba a kan lokaci yasa gabban jinsin guda biya suka ci gaba da girma a jikinta duk da cewa ta fi karkata ga mace.
An wayi gari Aisha tana al’ada kamar kowacce mace shiga shekarun balaga na ‘ya mace amma kuma ko kirgar dangi babu a tare da ita sannan kuma muryarta ta yi kaushi irin ta maza.
“Kullum ina cikin gida a daki saboda takaicin abin da jama’a za su ce min idan na fita waje. Hakan ne ya sa na daina zuwa makaranta da duk wani abu da zai hada ni da jama’a.”
Babban burin Aisha shi ne ganin ta wayi gari ta ga ‘ya’yanta wanda kuma tuni ta dauki hanya kasancewar ta samu saurayi kuma har ya tura mahaifansa domin a nema masa inda kuma tuni aka ba shi.
Wani karin burin da Aisha ke da shi shi ne samun ilimin zamani wanda kuma tuni ta dauki hanyar.