Babban Kwamitin Yada Labarai na JIBWIS Social Media, karkashin jagorancin Ustaz Ibrahim Baba Sulaiman ya bayyana rashin Shahararren Malamin Addinin musulunci, Sheikh Abubakar Abdullahi Giro Argungu a matsayin babban rashi da za a dade ba a maye gurbinsa ba.
Mataimakin Daraktan Kwamitin, Engr. Adamu Attahiru ne ya jagoranci tawagar domin wakilcin shugaban a yayin jana’izar malamin a jiya Alhamis, ya bayyana rasuwar Sheikh Giro a matsayin babban rashin da ba wai ga Iyalai, Kungiyar Izala, Jihar Kebbi ko Najeriya ba, ya shafi kasashen Afrika da ma wasu kasashen duniya.
Kazalika ya bayyana Marigayin a matsayin daya daga cikin malaman da suka bada gagarumar gudummuwa ga Kwamitin Social Media ta fuskoki daban daban.
Baya ga nuna alhini da jimami, Kwamitin ya gabatar da addu’ar Allah ya karbi dukkan ayyukansa na Alkhairi, tare da isar da sakon dimbin wadanda suka tura ta’aziyyar su ta hanyar yanar gizo zuwa ga Shugaban Kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau da tawagarsa da kuma iyalan marigayin.
Da yake maida nasa jawabin, shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ya nuna matukar godiya da wannan kwamitin kuma ya yi kira ga kwamitin na Social Media da su kara jajircewa saboda samun ladan da ake bayarwa ga wanda ya watsa Alkhairi kuma ya ja hankalin ‘yan kwamitin da cewa su fara zaqulo kafofin Social Media masu watsa barna domin Al’umma su nisance su.
Daga karshe ya yi wa mamacin Addu’ar samun Rahamar Allah.
Jibwis Nigeria