X

Rashin hakuri ya sa wani tsohon direba, ya kashe matarsa da wuka a jihar Adamawa

A ranar 1 ga Janairun 2022 ne rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta cafke wani magidanci Muhammed Alpha mai shekara 57 bisa zargin kashe matarsa Hamsatu mai shekara 40 da wuka.

Shi dai Muhammed direban motar haya ce kuma ya auri Hansatu shekaru 20 da suka wuce kuma suna da ƴaƴa takwas tare.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Sulaiman Nguroje wanda ya sanar da haka ranar Lahadi ya ce Muhammed ya kashe matarsa ranar da aka shiga 1 ga watan Janairun 2022 a kauyen Lande dake karamar hukumar Gombi.

Nguroje ya ce Muhammed ya aikata wannan aika-aika ne a lokacin da ya dawo gida ya iske matarsa Hansatu ta cire fallen falankin kofar gidan su ta saka a kofar ɗakin ta.

“Dama can Muhammed ya saki Hansatu saboda rashin zaman lafiya a auren su.

“Bayan sakin sai Hansatu ta nemi gida kusa da gidan tsohon mijinta tana zama.

Nguroje ya ce cikin fushi Muhammed ya dauki sharbebiyar wuka ya je ya caka wa Hamsatu a wuya nan take Hamsatu ta fadi jini na feso wa daga wuyan ta.

Ya ce dakacen kauyen Lande Malam Jauro Boka ya kawo karar abinda Muhammad yayi ofishin ‘yan sanda dake Gombi.

Nguroje ya ce Hansatu ta rasu bayan an kaita asibiti cikin gaggawa amma Muhammed na tsare a ofishin ‘yan sanda.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mohammed Barde ya bada umurnin gudanar da binciken abinda ya faru cikin sirri sannan ya hori mutane da su daina daukan doka a hannun su a duk lokacin da ransu ya ɓaci.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings