Shugaban kwamitin bincike na Rasha Alexander Bastrykin ya shaida wa wata jaridar gwamnatin ƙasar cewa akwai wasu kusan mutum 100 da ake nema ruwa a jallo.
Ya kuma zargi ma’aikatan kiwon lafiya na Ukraine ba tare da hujja ba, cewa suna samar da makaman ƙare dangi.
Mr Bastrykin ya bayar da shawarar kafa wata kotu ta musamman tare da samun goyon bayan kasashe da suka hada da Bolivia da Iran da Syria — ƙawayen Rasha.
Babu wani martani kawo yanzu daga ɓangaren Ukraine.
Akwai kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke gudanar da bincike laifukan yaƙi da ake zargin Rasha da aikatawa a Ukraine.
Zargin da Moscow ta musanta aikatawa.