Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano ta kama tsohon Kwamishinan ayyuka na Kano, kuma tsohon shugaban hukumar gyaran tituna Engr. Idris Wada Saleh.
Rahotonni sun ce hukumar ta cafke tsohon Kwamishinan ne bisa zargin badaƙalar kuɗi har Biliyan Guda da sunan gyaran titunan Kano da aka bai wasu kamfanoni guda uku North Stone Construction Company Nigeria Limited da Arfat Multiresources Limited da kuma 1st Step Construction Limited.
Hukumar dai na binciken yadda aka fitar da wannan kuɗi har Biliyan Guda ba tare da bin ƙa’ida ba.
Ta kuma zargi cewa, an lissafa wasu tituna da aka ce an yiwa gyara da kuɗin amma ko ƙasa ba a yayyafa musu ba.
Wata majiya a Hukumar Yaƙi da rashawan ta tabbatar da cewa an yi gaggawar sakin kuɗin a watan Afrilun wannan shekara, bayan da aka ayyana cewar Jami’yyar APC mai mulki a lokacin ta sha ƙasa a zaɓe.
Yanzu haka tuni ma’aikata suka soma bayar da shaida kan yadda aka basu umarnin gaggauta fitar da wannan kuɗi.