Tsohon shugaban hafsan soji na mulkin soja, Sani Abacha, Oladipo Diya ya rasu.
Diya ya rasu ya na da shekaru 79 a duniya.
Barista Prince Oyesinmilola Diya ne ya sanar da rasuwarsa a madadin iyalansa a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A madadin daukacin iyalan Diya gida da waje, muna sanar da Rasuwar Maigidanmu, Uba, Kakanmu, Ɗan’uwa, Laftanar Janar Donaldson Oladipo Oyeyinka Diya (Rtd) GCON, LLB, BL, PSC, FSS, mni.
“Daddynmu ya mutu a cikin daukaka a farkon sa’o’in 26 ga Maris 2023.”