A jiya ne gwamnatin jihar Ogun ta tabbatar da samun karin mutane hudu da suka kamu da cutar ta Monkey Pox, wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar zuwa bakwai.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Tomi Coker, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce an gano wasu kararraki guda biyu a Ota, a cikin karamar hukumar Ado-Odo/Ota, yayin da Abeokuta ta Arewa da Abeokuta ta Kudu ke da guda daya.
Sanarwar ta bayyana cewa Jami’an Sa-ido da Sanarwa da Cututtukan, DSNO, a kananan hukumomin da abin ya shafa sun gudanar da jerin layukan da suka shafi tuntubar juna, inda suka nuna cewa tuni majinyatan suna shan magungunan da aka rubuta.
Sannan kuma ta shawarci mazauna yankin da su guji cudanya da ruwan jiki kai tsaye ko ciwon rayayyun dabbobi ko matattun dabbobi, mutane ko gurbatattun abubuwa, kamar yadda ta jaddada wanke hannu da sabulu da ruwa akai-akai musamman bayan ziyara ko kula da mara lafiya.
Yayin da ya kara da cewa ya kamata a dafa kayan abincin dabbobi yadda ya kamata kafin a ci abinci, Coker ya yi kira da a kwantar da hankula daga mazauna yankin, yana mai tabbatar da cewa ana daukar matakan da suka dace don dakile yaduwar cutar.