Hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi ta kasa, ta sanar da damke wasu ‘yan kasan Chadi da Nijar – Shugaban hukumar, Buba Marwa, ya ce an kama su ne da laifin samar da miyagun kwayoyi ga ‘yan ta’addan kasar nan – A cewar Marwa, mutum miliyan 15 kuma masu shekaru 15 zuwa 60 ne kasar nan suke ta’ammali da miyagun kwayoyi
An cafkesu ne a makon da ya gabata a jihohin Taraba da kuma Nijar, Daily Trust ta ruwaito. Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana hakan a Abuja yayin da shi tare da kungiyarsa suka ziyarci ministan yada labarai da al’adu na kasar nan, Lai Mohammed. Marwa yace hukumar tayi nasarar damke masu safarar kwayoyi 2,175, an kwace kilogram 2,050,765.33 na miyagun kwayoyi tare da kwace magunguna da zasu kai darajar N75 biliyan. KU KARANTA: Ban sake bacci ba tun bayan da aka kashe sojoji a Benue, Ortom NDLEA ta damke ‘yan kasar Chadi da Nijar dake samarwa ‘yan ta’adda miyagun kwayoyi.
Ya ce ‘yan Najeriya dake da shekaru daga 15 zuwa 60 kusan miliyan 15 ne ke amfani da miyagun kwayoyi kuma kashi 25 duk mata ne. Ya ce wannan ziyarar sun yi ta ne domin neman goyon bayan ma’aikatar wurin yada labarai da wayar da kai ga masu ta’ammali da miyagun kwayoyi. A yayin martani, ministan yace, “Wannan tsanantar lamurran ‘yan bindigan da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a kasar nan ba zai rasa nasaba da miyagun kwayoyi ba da kuma illarsu ga jama’a.” A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi bayanin dalilin da yasa ya zabi Alkali Baba a matsayin sabon mukaddashin sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya. Bayan sanarwar da aka yi, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya kawata IGP a ranar 7 ga watan Afirilu yayin da Buhari yake kasar Landan domin duba lafiyarsa. Wannan sanarwan ta nadin sabon IGP ya janyo cece-kuce inda wasu ke ganin bai dace ba a kundin tsarin mulki.