X

Nan gaba kadan wahalar man fetir zata kau a Najeriya : NNPC

Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC, Mele Kyari, ya ba da tabbacin cewa wahalar da ‘yan ƙasar ke sha sakamakon ƙarancin fetur za ta zo ƙarshe nan gaba kaɗan. 

Mele Kyari ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da yake amsa gayyatar kwamatin Majalisar Wakilai da ke bincike kan yadda aka shigar da gurɓataccen man fetur Najeriya. 

“Game da matsalar nan, bari na ba ku tabbaci cewa mun ɗauki dukkan matakan da suka dace wajen dawo da shigo da mai ƙasar nan. Mun ba da oda mai yawan gaske da za ta ba mu damar kai wa cikin watan Maris, yayin da muke da lita biliyan 2.1 a yanzu,” in ji shi. 

“Matsalar da kuke gani, ina tabbatar muku cewa za ta zo ƙarshe nan da mako mai zuwa. Idan komai ya tafi lafiya, saboda matsalolin da ba za mu iya magancewa ba ciki har da jigilar mai a manyan motoci, ba don haka ba, muna da ingantaccen tsari na rarraba mai da zimmar fita daga wannan yanayin.”

Categories: Uncategorized
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings