MUTUWAR MUTUM 295 A KANO DA JIGAWA: An ɗora laifin ɓarkewar amai da gudawa kan rashin ruwa mai tsafta da yawaitar ƙazanta
An bayyana cewa amai da gudawa ya kashe mutum 295 a jihohin Kano da Jigawa a cikin wata ɗaya.
Yayin da Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Jigawa, Salisu Mu’azu ke bayani a ranar Laraba, ya shaida manema labarai cewa an samu rahotannin ɓarkewar cutar amai da gudawa fiye da sau 5,000 a jihar Jigawa, cikin watanni huɗu.
Wani jami’in lafiya a Jihar Kano, Bashir Lawan, ya ce ya zuwa ranar Laraba ɗin nan an samu rahotannin ɓarkewar amai da gudawa kusan sau 5,555 a cikin watan Maris a Kano.
Yadda Amai Da Gudawa Ya Rikita Jama’a:
Hassan Galadima shaida wa wakilin mu cewa ya rasa dangin sa biyu da matar yayan sa, A’isha Muhammad, mai shekaru 35.
“Da akwai kulawa da magani a asibitin sha-ka-tafi na Zareku, cikin Ƙaramar Hukumar Miga a Jihar Jigawa, to da wataƙila da sauran kwanan ta a gaba.”
Ya ce an kai ta cikin dare a ranar 29 Ga Yuli, amma lamarin ya kai gargara, jami’an lafiya su ka ce sai dai a tafi Jahun da ita. Tsakanin Jahun da Zareku kilomita 20 ne.
Ya ƙara da cewa washegari kuma ƙanwar sa Amina Galadima mai sheksru 16 ita ma amai da gudawa ya kashe ta.
“Ita a gida ma ta mutu, saboda mun san ko mun kai ta asibiti, babu maganin da za su yi mata.”
Galadima ya danganta ɓarkewar cutar kwalara kan rashin ruwan sha mai tsafta da kuma yawaitar ƙazanta barkatai. Sai kuma rashin jami’an kiwon lafiya da ƙarancin magunguna a asibitocin karkara.
Ya ce yawancin mutanen yanki su na samun ruwan sha ne daga bututun da ya lalace ko kuma ya yi tsatsa, duk kuwa da gargaɗin da jami’an kiwon lafiya su ke yi cewa a guji yin hakan.
Dagacin ƙauyen Zareku, Abdulƙadir Ibrahim ya ce mutum biyar sun mutu a garin a ranar Juma’a. Amma zuwa ranar Talata waɗanda su ka mutu sun kai mutum takwas.
Abubakar Idris daga Unguwar Kurna a Kano ya ce ya kai matar sa mai shekaru 41 da Adamu Ahmed daga Goron Dutse duk sun yi wa wakilin mu bayanin yadda cutar ta yi illa a gidajen su da unguwannin su.