An yi zargin cewa an jefe wani kabilar Oro har lahira a wata arangama da wasu mabiya cocin Truth and the Spirit Prophetic da ke Agege a jihar Legas a safiyar ranar Talata.
Lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani bawan gargajiya mai suna Agboola Akeem, ya samo asali ne sakamakon kutsawa cikin harabar cocin a lokacin da suke gudanar da bukukuwan nasu.
Rahotanni sun ce fada ya barke ne a tsakanin kungiyoyin biyu bayan da mabiya cocin suka ki amincewa da umurnin da masu ibadar Oro suka bayar na dakatar da gudanar da ibadarsu.
An kama shugaban cocin, wata mai suna Mercy Okocha mai shekaru 50 da wasu mutane tara da ake zargi.
Majiyar ‘yan sandan da ta tabbatar wa jaridar Vanguard haka bisa sharadin sakaya sunanta ta ce cocin da aka ambata yana lamba 2, Titin Taiwo Lawal a Oko Oba, Agege, jihar Legas.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin a shafin Twitter, ya ce “Masu ibadar kabilar Oro sun yi arangama da ‘yan cocin da ke gudanar da sintiri. Abin bakin ciki ya yi sanadiyar mutuwar mutum daya. A fili lamarin kisan kai ne. An kama wadanda ake zargi.”