X

MURIC Ta Ba Da Umarnin Binciken Tashin Bam A Kauyen Kaduna

Kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta dorawa gwamnatin tarayya alhakin gudanar da bincike kan harin bam da aka kai a kauyen Tudun-Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna kimanin mutane 120…

Kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta dorawa gwamnatin tarayya alhakin gudanar da bincike kan harin bam da sojojin Najeriya suka kai a kauyen Tudun-Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna kimanin mutane 120.

Farfesa Ishaq Akintola, Babban Darakta na MURIC ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba.

“Jiragen yaki marasa matuka sun kashe mutane 120 da ba su ji ba ba su gani ba a Tudun-Biri, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba. Wadanda abin ya shafa suna murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) ne a lokacin da wannan mummunan lamari ya faru.

“Ko da yake sojojin Najeriya sun amince da kai harin. Muna Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa mutanen kauyukan da ba su ji ba ba su gani ba. Lamarin ya nuna rashin kulawa da rashin kwarewa.

“MURIC na buƙatar cikakken bincike game da yanayin da ke tattare da wannan bala’i. Wadanda aka samu da hannu wajen kisan gillar da aka yi wa wadannan mutanen kauyukan Musulmi wadanda ba su ji ba ba su gani ba, dole ne a fuskanci fushin doka.
“Muna kuma neman cikakken diyyar rayukan da aka rasa da kuma asarar dukiyoyi a wannan harin na rashin tunani. Rayuwa abu ne mai tsarki kuma bai kamata sojoji su mayar da fararen hula marasa laifi su zama maharan halal na injunan kashe su ba,” inji shi. (NAN)

Categories: Labarai
Tags: Kaduna Bom
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings