X

Muna binciken bidiyon don sanin sihhancinsa game da  Kisan Fatima da ‘yayanta:Buhari

Daga karshe, fadar shugaban kasa ta yi tsokaci kan bidiyon kisan wata ‘yar Arewa da ‘yayanta a Anambra Shugaba Buhari ya ce ana kan gudanar da bincke kan bidiyon don sanin gaskiyar lamarin Shugaban kasan ya yi kira ga yan Najeriya kada su yi wani abu da zai tada tarzoma a cikin jama’a

Fadar shugaban kasa ta gargadi yan Najeriya kan yunkurin mayar da martani bisa bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta na kisan wata ‘yar Arewa mai juna biyu tare da ‘yayanta hudu. Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a jawabin da ya fitar ranar Laraba yace Shugaba Buhari ya kira ga yan Najeriya kada suyi gaggawan hukuncin kan bidiyon. Ya ce masana na gudanar da bincike kan bidiyon don sanin ko gaskiya ne ko ba gaskiya bane.

A cewar jawabin: “Fadar shugaban kasa na gargadi kan yunkurin tada tarzoma, lalata dukiya ko mayar da martani kan bidiyon da ake zargin yan kungiyar Eastern Security Network (ESN) da kashe yan ci rani.” “Yayinda masana ke gudanar da bincike kan gaskiyar bidiyon, muna kira ga yan Najeriya kada suyi gaggawan hukuncin da ka iya tada tarzoma.”

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da kashe-kashe mutane da akeyi a yankin kudu maso gabas da wasu sassan Najeriya.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings