Ɓangaren Abdul’aziz Yari da Sanata Kabiru Marafa sun yi watsi da buƙatar Gwamna Bello Matawalle ta neman raba muƙaman jam’iyyarsu ta APC da kuma na gwamnatinsa.
Abdul’aziz Yari wanda tsohon gwamnan Zamfara ne ya faɗa yayin wani taron manema labarai a Abuja cewa su ne ruhin APC a jihar don haka idan ba a su kaso mafi yawa na muƙamai ba, kamata ya yi a raba daidai.
A cewarsa, bayan tattaunawa a tsakani, ɓangarensu ya yanke shawarar cewa tayin da Gwamna Bello Matawalle ya yi musu, na su karɓi kashi 30% na muƙaman jam’iyya da gwamnati, ba abu ne mai yiwuwa ba.
“Mu da muke da jam’iyya, mun aminta cewa mu saki kashi 20% (na muƙamai) amma an ba mu shawara cewa a’a, mu yi shi hamsin, hamsin. Mu, mu saki kashi 50%,, shi kuma ya saki kashi 50%,” in ji Yari.
A cewar tsohon gwamnan: “Amma shi (Matawalle) yana cewa a’a sai dai ya ɗauki kashi 70% na jam’iyya, mu kuma ya sakar mana kashi 30%.
Sannan kuma ya ɗauki kashi 70% na gwamnati, (mu) kuma mu ɗauki kashi 30%. Ka ga….ai abin akwai matsala a ciki”.
Martanin ɓangaren su Yari ya zo ne bayan wata ziyarar ba-zata da Bello Matawalle ya kai wa Sanata Marafa ne cikin ƙarshen mako a gidansa na Kaduna, inda suka tattauna game da buƙatar raba muƙaman.
Abdul’aziz Yari dai ya ja hankali shugabancin uwar jam’iyyarsu ta APC da ke shiga tsakani cikin wannan lamari na raba muƙamai tun bayan komawar Gwamna Matawalle jam’iyya mai mulki a ƙarshen watan Yuni.
“Matsalar Zamfara fa ba irin matsalar Ebonyi ba ce, ba irin matsalar Kuros Riba ba ce. Jam’iyyar APC a Zamfara tana da komai, tana da gwamna, tana da sanatoci, tana da kowa, abin da ya faru mun sani,” cewar Yari.
Ko gobe idan aka yi zaɓe, muna da yaƙini za mu kai labari in ji shi. “To ba wai wani abu ne da take shakkun za ta iya faduwa ba. Ba wai mazaɓa ba, rumfa. Ba ta shakka!”.
A cewarsa, akwai tsari taƙamaimai a ƙasa da saɓa da na sauran jihohi. “A Ebonyi, ba ma iya cin rumfa, a Kuros Riba ba ma iya cin rumfa, amma tun da aka fara wannan mu’amalar muna iya cin kowannen irn zaɓe a jihar Zamfara. Kuma an kwata an gani,” in ji jigon jam’iyyar na APC.
Ya ce matsayin da suka gabatar wa gwamna Matawalle na raba muƙaman gwamnati da na jam’iyya daidai-wa-daida, shi ne mafi adalci a tsakanin ɓangarorin biyu.
“Ana ingiza wuta daga Abuja”
Tsohon gwamnan na Zamfara ya kuma zargi uwar jam’iyyar da rura wutar rikici a Zamfara ta hanyar ci gaba da ayyukan rijistar APC duk da umarnin kotu na cewa a dakata.
“Ita jam’iyya duk da an yi wannan, amma ta aika da kwamiti cewa ya je ya yi rijista, abin da kuma an hana ta. Haramtaccen abu ne saboda kotu ta ba da oda,” cewar Yari.
Ya ce odar ta samo asali ne bayan wasu ‘ya’yan jam’iyyar sun garzaya kotu, lokacin da shugaban kwamitin riƙon Mai Mala Buni ya sanar da rushe shugabancin APC daga mazaɓu zuwa ƙananan hukumomi.