X

MOPPAN ta sasanta Naziru Sarkin Waƙa da matan Kannywood

“Taron ya tattauna abubuwa da dama, daga baya aka yi nasiha da jan kunne gami da fadakarwa daga malamai,” in ji wata sanarwa daga MOPPAN.

Ta ci gaba da cewa: “Haka kuma taron ya yi bayanai na girmamawa ga Hajiya Ladin Cima da irin gudunmawar da ta bayar ga masana’antar fim da kuma ci gaba da lallashinta da girmama dukkanin dattijan masana’antar da guje wa yin lafazi maras kyau a kan su.”

An yi zaman sulhun ne ƙarƙashin ƙungiyar MOPPAN da haɗin gwiwar AFMAN a zauren taron Kannywood TV da ke birnin Kano jiya Litinin, inda aka yi sasanta tsakanin Naziru M Ahmad (Sarkin Waka) da kuma ƙungiyoyin mata na Kannywood. 

Daga cikin Dattawan da suka halarci taron, akwai Malam Auwalu Masha, Mai’unguwa Ibrahim Mandawari, Ibrahim Gumel, Kabiru Maikaba.

Lamarin ya ƙara zafafa ne bayan da Sarkin Waƙa ya yi zargin cewa ana yin lalata da wasu mata kafin a ba su damar saka su a fim sannan kuma ba a biyan wasu haƙƙinsu, abin da ya jawo martani da dama.

Wasu ƙungiyoyin mata na Kannywood kamar ‘K-WAN’ sun nemi Nazirun da ya janye kalamansa ko kuma su kai shi kotu.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings