Yan bindiga sun sake kai hari kasuwar garin Goronyo, a jihar Sokoto, karo na uku cikin mako biyu Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi, inda suka kashe mutane da dama Yan bindiga na cigaba da tserowa zuwa jihar Sokoto daga Zamfara, inda jami’an sojoji ke luguden wuta ta sama da ƙasa kan yan ta’addan.
Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari kasuwar garin Goronyo dake ƙaramar hukumar Goronyo, a jihar Sokoto. Wata majiya daga garin ta bayyana cewa yan ta’addan sun kai hari da adadi mai yawa na mutane ranar Lahadi da daddare, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi. Rahoto ya nuna cewa har zuwa yanzun ba’a san adadin yawan mutanen da harin ya shafa ba, amma mutane da dama sun mutu.
Wannan harin shine karo na uku cikin mako biyu da yan bindiga suka kai wata kasuwa a jihar Sokoto.
A wani rubutu da shafin Daular Usmaniyya ta buga a dandalin Facebook, ta jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa. Wani sashin rubutun yace: “Muna mika ta’aziyya ga al’ummar musulmi na jahar Sokoto, musamman na Karamar Hukumar Goronyo akan Ibtala’in da ya faru na kisan kan mai uwa da wabi da ‘yan bindiga sukayi a kasuwar Goronyo.” Yan bindiga sun kashe mutum 20 A farkon wannan watan ne, wasu tsagerun yan ta’adda suka hallaka aƙalla mutum 20 a kasuwar Ungwan Lalle, ƙaramar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto. Sojoji sun kwashe makonni da dama suna aikin ruwan wuta ta sama da ƙasa kan sansanin yan bindiga a jihar dake makotaka da Sokoto, wato Zamfara.