Wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga tare da kashe wata daliba da ke karatu a Kwalejin Shehu Shagari ta Jihar Sakkwato kan zargin yin batanci ga Manzo (S. A.W).
Jaridar Leadership ta rawaito cewa Matasan nan take suka farwa dalibar, suka yi mata dukan tsiya, suka kashe tare da kone gawarta, suka kuma dore gawar suka yi ta janta a titi kamar yadda hotuna da bidiyon faruwar al’amarin ya nuna.
Wasu rahotanni sun tabbatar da Jami’an tsaron ‘Yan Sanda sun je Kwalejin don kwantar da tarzomar sakamakon abun da ya faru.
Lamarin ya dauki hankalin Jama’a da dama sai dai har yanzu bamu ji ta bakin mahukata a makarantar ba kawo yanzu da muke hada wannan rahoton.