X

Manyan ‘yan ta’adda sun tsere daga gidan yarin Kenya

Rundunar ‘yan sandan Kenya ta ce, manyan ‘yan ta’adda uku sun tsere daga wani gidan yarin kasasr ciki har da wanda aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 41 saboda samun shi da laifi a harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 148.

Sashen binciken manyan laifufuka a rundunar ‘yan sandan kasar ya sanar da ware Dala dubu 535 ga duk wanda ya taimaka da bayanai don cafke  mutanen wato Mohamed Ali Abikar, Joseph Juma Odhiambo da kuma Musharaf Abdalla Akhulunga da suka tsere daga gidan yarin mafi tsaro a kasar da ake kira Kamiti a wajen birnin Nairobi.

Hukumomin Kenya ba su yi bayani ba kan yadda manyan ‘yan ta’addan suka tsere daga gidan yarin na Kamiti mai cike da tsaro.

Kodayake Kwaminishinan Kula da Gidajen Yarin kasar, Wycliffe Ogallo ya ce, ya ziyarci gidan kason domin tantance yadda ‘yan ta’addan suka tsere.

Ogallo ya gargadi jama’a da su kauce wa samar da matsugumi ga wadannan mutane masu cike da hadari.

Categories: Labarai
Tags: HAUSAlabarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings