Ƙasuwar ‘yan ƙwallo: Makomar Sterling, Vlahovic, Zidane, Pochettino, Rangnick, Milinkovic-Savic, Perisic,
Manchester City za ta dage domin ganin ta sa Raheem Sterling ya tsaya a kungiyar, ganin cewa ana danganta dan wasan na Ingila mai shekara 26 da tafiya Barcelona wadda ake cewa za ta ba shi kwantiragi mai tsawo. (Telegraph)
Manchester United ta bi layin kungiyoyi da dama da suka hada da Tottenham da Newcastle United, wajen son sayen dan wasan gaba na Serbia Dusan Vlahovic mai shekara 21 daga Fiorentina. (Mail)
Paris St-Germain ta tattauna da Zinedine Zidane a shirin da kungiyar take yi na rabuwa da kociyanta Mauricio Pochettino wanda Manchester United ke nema. (Le Parisien daga Metro)
Ralf Rangnick ya yarda ya zama kociyan rikon kwarya na Manchester United bayan da daga farko ya ki amincewa, sai bayan da kungiyar da Old Trafford ta sake tsarin kwantiraginl. (Manchester Evening News)
Duk da yuwuwar zuwan Rangnick Manchester United na son Pochettino ya kasance kociyanta a bazara mai zuwa. (90 Min)
Dan wasan tsakiya na Lazio Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 26, ne Manchester United ke harin dauka domin maye gurbin Paul Pogba, wanda kwantiraginsa da kungiyar ta Old Trafford zai kare a bazara. (Fichajes)
Barcelona na shirin neman dan gaban Basel Arthur Cabral amma kuma sai ta sayar da wasu ‘yan wasa kafin ta yi maganar sayen dan Brazil din mai shekara 23. (Goal)
Kwantirgin dan wasan gaba na gefe na Croatia Ivan Perisic a Inter Milan zai kare a watan Yuni na 2022 kuma dan wasan mai shekara 32 ya ce komai zai iya faruwa a cikin ‘yan makwanni, da aka tambaye shi a game da makomarsa (Mediaset Infinity daga Football Italia)
Inter Milan na fatan dan wasanta na tsakiya dan Croatia Marcelo Brozovic zai kulla sabon kwantirgi da ita kasancewar kwantiraginsa na yanzu zai kare a bazara. (90 Min)
Kociyan AC Milan Stefano Pioli, mai shekara 56, zai kulla sabon kwantiragi na shekara biyu da kungiyar ta Italiya a ranar Juma’ar nan. (Calciomercato, daga Football Italia)