Gwamnatin tarayya ta ware kudi N460,217,071 na ‘Kayayyaki’ na Majalisar Jiha a cikin Kudirin Kasafin Kudi na 2024.
Daga cikin jimillar, kayan abinci za su ci N253,277,638
Sauran abubuwan da ke ƙarƙashin babban jigon sun haɗa da kayan abinci, kayan rubutu, jaridu, da littattafai, da sauransu.
Hakan na kunshe ne a cikin takardar kudirin kasafin kudin da ofishin kasafin kudi na tarayya ya fitar ranar Laraba.
Shugaban kasa Bola Tinubu ne ya gabatar da kasafin kudin ga zaman hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar a ranar 29 ga watan Nuwamba.
Tinubu ya yi wa kundin kasafin kudi Lakabi da “Budget of Renewed Hope.”