X

Majalisa ta umarci Hukumar Kwastan ta biya diyyar Naira miliyan 360 ga iyalan mutum 18 da ta bindige

Majalisar Tarayya ta amince da rahoton kwamiti, wanda ya umarci Hukumar Kwastan ta Ƙasa ta biya diyyar Naira miliyan 360 ga iyalan mutum 18 da jami’an ta suka kashe a Katsina da Oyo.

Sannan kuma ta yi kira da a gurfanar da dukkan jami’an kwastan ɗin da ke da hannu a kisan, domin a hukunta su.

Daga cikin kuɗaɗen za a biya Naira miliyan 200 ga iyalan mutum 10 da kwastan su ka kashe a Jibiya, Jihar Katsina.

Sannan kuma Majalisa ta umarci a biya diyyar Naira miliyan 160 ga mutum 8 da su kwastan ɗin su ka kashe a Jihar Oyo.

Majalisar Tarayya ta yanke shawarar umartar kwastan su biya diyyar, bayan Kwamitin Lura da Hukumar Kwastan ya bayar da sakamakon binciken da ya gudanar.

Kwamitin ya bi diddigin yadda kwastan suka yi kisan, kuma ya bayar da rahoton sa a ranar Talata.

Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya Idris Wase ne ya jagoranci zaman, kuma ya amince da rahoton da Shugaban Kwamitin Kwastan Leke Abejide daga Jihar Kogi ya gabatar, a ranar Talata.

Taɓargazar Kwastan A Katsina:

A cikin Agusta 2021 ne jami’an kwastan a Katsina suka rimtsa motar su ƙirar Hilux a cikin gungun wasu mutane da ke zaune gefen titi a garin Jibiya, suka kashe su.

Daga nan Danmajalisa Sada Soli Jibiya ya tayar da maganar a kotu, kuma ya nemi a yi bincike.

Kwastan sun afka a kan mutanen ne a Jibiya, a lokacin da su ke bin wasu ‘yan sumogal ɗin shinkafa a guje.

Saboda haka ne Kwamitin Abejide ya ce a biya Naira miliyan 20 ga iyalan kowane mutum ɗaya da kwastan ɗin su ka kashe su 20. Sannan kuma su biya Naira miliyan 2 ga kowane mutum daga mutum 13 da kwastan suka ji wa raunuka.

Sauran waɗanda za a biya diyyar kuma a jihar Oyo su ke, waɗanda aka kashe a Iseyin. Kwamiti ya Naira miliyan 80 ga iyalan mamatan da kwastan suka kashe. Sai kuma Naira miliyan 2 ga waɗanda suka ji ciwo.

Akwai kuma waɗanda kwastan suka kashe a Igangan da Tapa. Su ma za a biya su diyyar Naira miliyan 80 da Naira miliyan 2 diyya da kowane da aka ji wa rauni.

Majalisa ta yi kira ga Hukumar Kwastan da su shiga taitayin su, kuma su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya, domin su kyautata alaƙar su da jama’a fararen hula.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings