X

Mahara sun kai hari ofishin yan sanda Nkporo, sun saci AK-47

Rundunar ‘yan sandan jihar Abia ta ce wasu ‘yan bindiga sun sace akalla bindiga kirar AK-47 guda daya dauke da alburusai 30, Kayan Yansada biyu da wasu alburusai da dama da suka sace a yayin kai hari a hedikwatar ‘yan sanda ta Nkporo da ke yankin Ohafia ranar Lahadi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Geoffrey Ogbonna, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ’yan bindigar da ke aiki a cikin motocin Toyota Sienna guda uku sun yi harbe-harbe, suka kori jami’an ‘yan sanda da ke bakin aiki, suka kutsa cikin rumbun ajiye makamai na tashar tare da sace kayayyakin.

Ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da wasu kakin da aka ajiye a ma’ajiyar kayan yaki da ofisoshi tare da jikkata wasu ‘yan sanda uku.

Ya kara da cewa, “Duk da haka, cikin hanzarin hadin gwiwa da ‘yan sanda da sojoji suka yi, ya sa aka yi watsi da wata mota kirar Toyota Sienna, tare da wasu kayan aikin hidima, da takalma da sauran abubuwan da aka kwace daga hannun ‘yan sandan.

“An kwantar da biyu daga cikin ‘yan sandan da suka jikkata a asibiti yayin da daya ke jinya aka sallame su.”

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings