Wata kotu a kasar Libya ta janye haramcin tsayawa takara a zaben shugaban kasa da hukumar zabe kasar ta yi a kan Seif al-Islam Gaddafi dan tsohon Shugaba Marigayi Moammar Gaddafi.
Kotun da ta yi zamanta a yankin kudancin Sabha, ta yanke wannan hukunci ne a jiya Alhamis bayan da aka kwashe kusan mako guda ana dauki ba dadi tsakanin ma’aikatan kotu da wasu mutane dauke da manyan bindigogi da suka hana zaman kotun.
A makon da ya gabata ne hukumar zaben kasar ta yi amfani da zaman gidan yarin da Seif al Islam Gaddafi ya yi ta soke takardunsa na takarai, lamarin da ya kai shi ya garzaya zuwa kotu.
Za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasar ne a ranar 24 ga wannan wata na Disamba da muke ciki. an fata wannan zaben ya kawo karshen shekaru da kasar ta Libya da ke yankin arewacin Afirka ta tsinci kanta a hali na rikici tun bayan hambarar da gwamantin Marigayi Moammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40.