Wata tawagar matasan lauyoyi 31 na Arewacin Najeriya sun kuduri aniyar taimakawa wajen goyon baya da kariyar mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari, da ke fuskantar tuhuma a kasar Amurka.ABUJA, NIGERIA —
A wani taron manema labarai da suka gudanar a Kaduna, wasu matasan lauyoyi 31 daga Arewacin Najeriya sun ce za su ba da ayukan kariya kyauta ga DCP Abba Kyari, musamman tsare ‘yancin sa da ake kokarin dannewa ta hanyar ikirarin da wata kotun kasar Amurka ta yi na samun sa da laifi.
Mai Magana da yawun lauyoyin 31, Barista Sanusi Bappah Salisu ya ce za su yi nazarin dukan matakan da hukumar binciken Amurka ta FBI ta dauka har ta kai kotun kasar ta tuhumi Kyari da aikata laifi a shari’ar da ake yi wa dan damfarar yanar gizo Ramon Abbas, da aka fi sani da Hushpuppi.
Ya ce haka kuma za su gabatar da tambayoyi akan yiwuwar take ‘yanci da hakkin Kyari, bisa tanadin kashi na 6 da na 7 na yarjejeniyar babban taron Afirka akan ‘yancin dan adam, wanda ya yi tanadin cewa kowane mutum yana da ‘yancin samun tsaron kan sa, kuma kowane mutum na da ‘yancin a saurare shi.
Sanusi ya ce lauyoyin sun kuduri aniyar bin kadin hakkokin Abba Kyari a duk tsawon wannan kiki-kakar, domin tabbatar da cewa ba’a danne masa hakki da ‘yanci ba a nan gida Najeriya da kuma a kasar Amurka.
Ya ce tawagar ta su ta sa kai, ta kumshi lauyoyi daga dukkan jihohi 19 na Arewacin Najeriya, da suka fito daga kabilu da addinai daban-daban.
Wannan dai na zuwa ne bayan wani taro da gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya suka gudanar, inda suka nuna yatsa akan wasu al’amura da suke gani tamkar sun sabawa tsare-tsaren kasa-da-kasa, a yunkurin hukumar FBI na cusa Abba Kyari a cikin dambarwar shari’ar Hushpuppi, da kuma gaggawar da hukumar ‘yan sanda ta yi na cire shi daga mukaminsa da kuma maye gurbinsa.
A kan haka ne kungiyar ta yi kira ga lauyoyin yankin na Arewa da su hada kai domin tabbatar da ganin ba’a danne hakki da ‘yancin Abba Kyari a cikin Najeriya da wajenta ba.