X

Labaran Yammacin Yau

Kotun sauraron kararrakin zabe a Jihar Kano ta kori karar tsohon Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Gaya na APC, inda ta tabbatar wa Kawu Sumaila na NNPP kujerarsa.

An daka wawa kan motoci 3 dauke da shinkafar da za a raba tallafi a Kwara.

Kotun zaɓen ƴan majalisar tarayya mai zamanta a birnin Jos, jihar Plateau, ta sauke Gyengdeng da ke wakiltar Barkin/Riyom a majalisar wakilai ta baiwa LP.

Wadansu mutane guda 4 da ake zargin masu tonon ma’adinai ta barauniyar hanya ne sun rasa rayukansu a jihar Bauchi, a cikin ramin da suke tonon ma’adinan.

Gwamnan Jihar Sokoto ya Kaddamar da motocin sufuri 140, sannan 20 domin zirga-zirgar mata zalla inda za su biya Naira 100 kacal don kai su duk inda suke so acikin jihar.

Wani jirgin ruwan yaƙin Birtaniya, ya sauka a Lagos don taimakawa wajen yaƙi da haramtattun ayyuka ciki har da fashin teku da fasa-ƙwauri a tsakanin ƙasashen yankin.

Da sanyin safiyar yau Litinin, wani lamari mai ban tsoro ya faru a gadar Mile 2 da ke jihar Legas, yayin da wata mata da har yanzu ba a tantance ba ta fadi ta mutu.

Ƴan bindiga sun halaka mutum 2 tare da yin awon gaba da wasu mutum 7 a ƙauyen Kwarikwarasa na jihar Kebbi Gwamnan jihar Kebbi ya ziyarci inda lamarin ya auku, sannan ya bayar da kyautar naira miliyan 10 ga waɗanda harin ya ritsa da su

Wani sabon hari da aka kai a kauyen Kulben da ke karamar hukumar Mangu na jihar Plateau ya hallaka mutane 11.

Adadin wadanda suka rasu a sanadiyar girgizar kasar Maroko, ya kai 2,500, a dai-dai lokacin da kasar ke naman gudunmuwar kasashe don kubutar da ragowar mutanen da ke makale a karkashin burabuzai.

Dubai ta ɗage haramcin bai wa ‘yan Najeriya biza

Shugaban Faransa ya sake tabbatar da cewa Shugaban Nijar Mohamed Bazoum kadai zai umartar janyewar sojojin Faransa daga yankin Sahel na Nijar.

Shugaban Faransa Bazoum ne kadai zai iya janye sojojinmu daga Nijar.

An saka dokar ta-ɓaci a Libya bayan ambaliya ta kashe mutum 150.

An tabbatar da mutuwar mutum 4 da kuma jikkatar wasu da dama bayan wata fashewa da afku a wani wajen haƙar ƙasa na China a Ghana.

Jami’an tsaro a yankin kudu maso yammacin Pakistan sun bazama neman ‘yan wasan kwallon kafa 6, a cewar ministan harkokin cikin gida na kasar.

Gwamnatin rikon kwaryar Nijar ta sallami Shugaban hukumar ‘yan Sanda akan wasu kalamai

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings