X

Labaran Talata 09/08/2022CE – 11/01/1444AH Ga Takaitattun labaran.

Kotu Ta Ware 7 Ga Satumba A Matsayin Ranar Fara Shari’a Kan Takardun Bogin Tinubu.

Hukumar EFCC ta kama wani mutum da ke zambar daukar aiki a Abuja.

Ohanaeze ta caccaki Buhari kan maganar da ya yi a kan rashin tsaron kudu maso gabas.

Amotekun ta kama mutum 320 da ake zargin da karya doka da suka taso daga Arewa.

‘Yan bindiga sun sace sirikan sanata a Katsina da ‘ya’yanta biyu.

Hukumar Shirya Jarabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta ce kaso uku cikin hudu na daliban da suka zana jarabawar kammala sakandare a bana sun ci darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi, bayan ta saki sakamakon jiya Litinin.

Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Ahmed Idris Wase, ya tabbatar wa al’ummar mazabarsa da ke fuskantar hare-haren ’yan bindiga cewa nan da makonni kadan za a kawo karshen kalubalen tsaro.

Wani dattijo yayi bayanin Yadda ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar ‘ya’yansa uku a jihar Jigawa.

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Daura yace yabar APC ne saboda an zagi ‘ya’yan Shugaba Buhari.

Kungiyar ASUU Ta Bukaci Soke Jarrabawar Jami’ar Jihar Kaduna.

An gurfanar da wani tsoho mai shekaru 80 mai suna Ayoola Adeqole ranar Litinin a gaban kotun Majistare da ke Ile-Ife a jihar Osun, bisa tuhumarsa da barazanar kashe wata mata.

Wani Dalibin Sakandire Ya Hada Mutum-Mutumi Mai Motsi A Kano.

Amurka ta bayyana bai wa Ukraine sabon tallafin tsaro da ya kai na dala biliyan daya, wanda ya kasance tallafi mafi girma tashi daya ta amfani da ikon shugaban kasa.

Hukumomi a Cuba sun ce wata gobara, ta kone motoci uku makare da danyen mai, a tashar jiragen ruwan birnin Matanzas da ke arewacin.

FBI ta kai samame gidan tsohon shugaban Amurka Donald Trump na Mar-a-Lago.

Mabiya mazhabar Shi’a sun zargi jami’an tsaro da kashe musu mambobi guda shida yayin muzaharar ranar Ashura ta bana a Zariyan jihar Kaduna.

Yayin da babbar kungiyar ’yan adawar kasar Chadi ta bijire wa sulhu da gwamnatin sojin kasar, sauran kungiyoyin su 40 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a kasar Qatar.

Categories: Labarai
Tags: HAUSAlabarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings